A jiya Talata ne, aka zartas da takarda a yayin taron musamman kan batun miyagun kwayoyi na shekarar 2016 na MDD. Kasashe daban daban sun yi alkawarin kara kokarin tinkarar batutuwan lafiya da tsaro da miyagun kwayoyi suka haifar, da kuma kara yin hadin gwiwa a kan wannan aiki.
Lokacin da aka bude wannan taro na musamman ba da dadewa ba, aka zartas da takarda mai taken "alkawarin daidaita batun miyagun kwayoyi", inda kasashe daban daban suka nanata alkawarin bisa yarjejeniyar hana yaduwar miyagun kwayoyi, kana sun dora muhimmanci kan batutuwan lafiya da tsaro da miyagun kwayoyi suka haifar, sun yi niyyar hana yin amfani da miyagun kwayoyi da kuma samarwa tare da sayar da su.
Takardar ta ce, "muna ganin cewa, ko da yake mun samu sakamako mai kyau a wasu fannoni, amma batun miyagun kwayoyi na ci gaba da kawo barazana ga lafiya da tsaro da kuma zaman rayuwar mutane. Mun yi niyyar kara yin hadin gwiwa wajen tinkarar wannan kalubale."(Lami)