Ministoci daga babbar kungiyar 'yan kasuwa ta kasashen Afrika COMESA, sun bukaci kasashen nahiyar ta Afrika wadanda ba su rattaba hanuun kan shirin TFTA ba da sanya hannu kan yarjejeniyar.
An kaddamar da shirin na kasuwanci ba tare da shamaki ba wato TFTA ne, a watan Yunin shekarar da ta gabata wanda kasashe mambobin na kungiyoyin COMESA da EAC da SADC suka kaddamar a garin Sharm el-Sheikh na kasar Masar.
Shirin ya kunshi mambobin kasashe Afrika 26 daga dukkan shiyyoyi uku wanda ya shafi al'umma sama da miliyan 625, da kuma yawan GDP da ya kai dalar Amurka triliyan 1.3.
Bayan kammala taronta a Lusaka, babban birnin kasar Zambiya, majalisar ministocin ta COMESA ta bayyana damuwarta kan kasancewar kasashe 16 ne kadai suka rattaba hannu kan yarjejeniyar daga cikin kasashe 26 na kungiyar.(Ahmad Fagam)