in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi kira da a kafa yankin kasuwanci maras shinge a Afirka
2015-04-10 14:18:18 cri

Taron ministocin kasuwanci da na 'yan majalisun Afrika, da ya gudana a ranakun Laraba da Alhamis a birnin Marrakech dake kudancin kasar Morocco bisa tsarin bukukuwan cikon shakaru 20 da kafa kungiyar kasuwancin duniya (WTO), ya kammala tare da wani kiran kara rubanya musanya tsakanin kasashen Afrika da kuma kafa wani yankin kasuwanci maras shinge na nahiyar.

A cewar wadanda suka shirya taron, musanyar kasuwanci tsakanin kasashen Afrika, da yawancinsu kananan kasashe ne da karfin tattalin arzikinsu ya kasance takaitace, ya sanya nahiyar Afrika kasancewa daya daga cikin nahiyoyi mafi rarrabuwa da mafi rashin ci gaban tattalin arziki a duniya.

Wannan matsala na ci gaba da kasancewa wani babban rauni ga tattalin arziki, lamarin da ke takaita hanyoyin samun bunkasuwar kasashen Afrika da rage karfinsu a cikin shawarwarin kasuwancin kasa da kasa.

Mahalarta taron sun nuna cewa, kafa wannan yankin kasuwanci cikin 'yanci na nahiyar zai taimaka wajen bunkasa kasuwancin Afrika, da kuma samar da kyakkyawar dunkulewar nahiyar Afrika a cikin tattalin arzikin kasa da kasa.

Bisa wannan tunani, ministan kasuwancin kasar Morocco, Moulay Hafid Elalamy ya nuna damuwa cewa, nahiyar Afrika, da ke kunshe da kashi 16 cikin 100 na yawan al'ummar duniya, na wakiltar kashi 3 cikin 100 na musanyar kasuwancin kasa da kasa, amma kuma ya jaddada cewa, haka nahiyar na samar da damammaki masu tarin yawa da za su ba ta damar kamo gibinta. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China