in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta bukaci a gudanar da kawasunci maras shamaki tsakanin kasashen duniya
2015-12-04 09:55:43 cri

Shugabar kwamitin kungiyar hada kan kasashen Afrika AU, Nkosazana Dlamini Zuma, ta ce, kasashen nahiyar Afrika za su gamsu da zarar aka cimma yarjejeniya a taron ministocin kasashen duniya kan cinikayya wato WTO a birnin Nairobi cewar za'a gudanar da harkokin cininkayya tsakanin kasashen duniya ba tare da shamaki ba.

A yayin wata hira da kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua a Pretoria, Dlamini Zuma, ta ce, suna ci gaba da tattaunawa kan ajandar taron ministocin kasashen, da nufin cimma matsaya don kawar da duk wani shinge a sha'anin harkokin kasuwanci.

Ana sa ran ministocin kudi da na harkokin wajen kasashen Afrika za su gudanar da taron a Nairobi, inda a yayin taron, ake sa ran daddalewa na shin ko za'a amince da batun gudanar da kasuwanci ba tare da shinge ba. Za a gudanar da taron ne tsakanin ranakun 15 zuwa 18 ga wannan wata na Disamba.

Tun gabanin taron, tuni kasar Sin ta yi alkawarin tallafawa kasashen na Afrika, ta yadda za su ci gajiyar sabon tsarin amfani da kudaden Renminbi wajen ci gaban kasuwanci a tsakanin bangarorin biyu.

Sannan kasar Sin, za ta tallafawa kasashen Afrika ta fuskar inganta masana'antu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China