An shirya taron ayyukan yin gyare-gyare kan tsarin tattalin arzikin kasar Sin na shekarar 2016
Kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin ya shaidawa manema labaru a yau Asabar cewa, a kwanan baya an shirya taro game da ayyukan yin gyare-gyare kan tsarin tattalin arzikin kasar na shekarar 2016, inda aka tabbatar da wasu muhimman fannoni da za a mai da hankali a kai, ciki har da zurfafa yin kwaskwarima kan masana'antu, ci gaba da rage hukumomin gwamnati da mayar da iko ga masana'antu, kara yin kwaskwarima kan tsarin zuba jari da na tattara kudi, inganta yin gyare-gyare kan farashin kaya, kana da kyautata tsarin raya birane da garuruwa, kafa sabon tsarin tattalin arziki na bude kofa, kyautata tsarin inganta yin kirkire-kirkire, da kuma inganta yin kwaskwarima kan tsarin halittu. (Bilkisu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku