in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A kalla mutane 8 ne suka rasu sakamakon harin Bam a tsakiyar Somaliya
2016-03-31 20:38:08 cri
A kalla mutane 8 ne aka tabbatar sun hallaka, sakamakon tashin wani bama a Otel din Unlay, dake garin Galkalcyo na yankin Mudug, dake arewa maso tsakiyar kasar Somaliya.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, harin na yau Alhamis ya rutsa da shugaban sashen kudi na jihar Puntland Sa'id Ali Yusuf, da wasu masu tsaron lafiyar sa su 5.

Kawo yanzu dai babu cikakkun bayanai daga mahukuntan kasar game da harin, sai dai mayakan kungiyar Al Shabab, sun ce su ne suka kaddamar da shi. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China