in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun AU a Somaliya sun kwace yankuna daga hannun Al-Shabaab
2016-04-05 10:07:15 cri
Dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika dake kasar Somaliya, AMISOM, wadanda ke samun tallafin sojojin gwamnatin Somaliya, a Litinin din nan sun yi nasarar sake kwace ikon garin Janale dake kudancin kasar a hannun mayakan Al-Shabaab.

Abdi Ibrahim Shamow, shi ne kwamandan 'yan sandan yankin Shabelle inda a can ne garin Janale yake, ya ce, tun da safiyar Litinin ne dakarun na hadin gwiwa suka kwace ikon garin daga hannun mayakan Al-Shabaab cikin ruwan sanyi.

Ya kara da cewa, mayakan Al-Shabaab sun yi yunkurin musayar wuta da dakarun na AMISOM, amma sun gagara, lamarin da ya sa suka fice daga garin babu shiri, sai dai ba a samu zub da jini ba a wannan karo.

A 'yan kwanakin nan dakarun hadin gwiwar suna ta gudanar da sintiri a yankunan.

A watan Satumban bara ne, mayakan Al-Shabaab suka kaddamar da mummunan hari kan dakarun na AMISOM a sansaninsu dake Janale, lamarin da ya haddasa mutuwar sojoji 70.

Kungiyar mai tsattsauran ra'ayin Islama ta jima tana fafatawa da dakarun gwamnatin Somaliya tare da kuma kaddamar da hare-hare a fadin kasar. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China