in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Somaliya ya yi kira da a hada gwiwa don yakar ta'addaci
2016-03-06 13:47:57 cri
Shugaba Hassan Sheikh Mohamoud na kasar Somaliya ya yi kira ga 'yan kasar da su baiwa jami'an tsaro hadin kai don ganin an murkushe ayyukan ta'addanci a kasar.

Shugaba Mohamoud ya bayyana hakan ne yayin da ya ke jawabi a wani taron dandalin harkokin tsaro da aka shirya a birnin Mogadishu, fadar mulkin kasar. Yana mai cewa, yanzu haka kasar tana yaki ne da kungiyar Al-Shabaab wadda ta kasance babbar barazanar tsaro ga al'ummar duniya baki daya.

Ya kuma bayyana cewa, nan ba da dadewa ba gwamnati za ta warware jinkirin da aka samu na biyan albashin sojojin kasar, duk da matsalar karancin kudin da gwamnatin ke fama da shi.

Shugaban na Somaliya ya kuma yi maraba da shawarar da majalisar zartarwar kasar ta gabatar a wannan mako game da matakan tsaron da ya kamata a dauka na rage hare-haren da kungiyar Al-Shabaab ke kaddamawar a sassan kasar.

Kalaman shugaban na zuwa ne yayin da kungiyar Al-Shabaab mai alaka da Al-Qaida ta kara zafafa hare-haren da ta ke a makon da ya gabata, hare-haren da suka yi sanadiyar rayukan mutane da dama, galibinsu fararen hula.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China