in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta gaza tantance adadin mutanen da rikici ya daidaita a yankin Darfur
2016-02-23 10:25:09 cri
MDD ta ce ba ta kai ga tantance hakikanin adadin mutunen da rikicin baya bayan nan a tsakiyar Darfur na kasar Sudan ya raba da matsugunan su ba.

Mai magana da yawun MDD Stephane Dujarric, ya shedawa 'yan jaridu cewar, hakan ya faru ne bayan barkewar wani sabon rikici a yankin Jebel Marra a tsakiyar watan Janairu, kamar yadda ofishin ba da jin kai na MDD wato OCHA ya tabbatar da hakan.

A makon da ya gabata, wata karamar tawagar jami'an ba da agaji ta isa yankin Nertiti dake tsakiyar Darfur, sannan sauran hukumomin ba da agaji na duniya suna birnin Zalingei amma a cewar Dujarric, jami'an ba su samu damar kaiwa ga yankunan da mutanen da rikicin ya tilasta su barin gidajensu ba.

MDD da takwarorinta sun bukaci hukumomi a kasar da su dauki matakan ba da dama ga jami'an domin su samu kaiwa ga yankunan tsakiyar Darfur, domin gano hakikanin adadin mutanen dake bukatar kai musu kayayyakin jin kai.

MDD ta yi kiyasin mutanen dubu 85 mafi yawansu mata da kananan yara ne rikicin Jebel Marra ya daidaita, a makonni biyar da suka gabata a arewacin Darfur wanda ke makwabtaka da tsakiyar Darfur. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China