in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta damu kan tashin hankalin da ke faruwa a yankin Darfur
2016-01-28 10:30:05 cri

Ofishin kula da harkokin jin kai na MDD da ke aiki a kasar Sudan, ya bayyana damuwa game da yadda tashin hankalin da ke faruwa a yankin Darfur ya ke tilastawa dubban fararen hula barin gidajensu.

Wasu rahotannin baya-bayan da ofishin ya fitar, sun yi nuni da cewa, fadan da ke faruwa a tsaunin Jebel da ya hade jihohin Darfur guda uku ya tilastawa kimamin fafaren hula 19,000 tsallakawa zuwa jihar arewacin Darfur, baya ga wasu 15,000 da suka shiga jihar Darfur ta tsakiya.

Wata sanarwa da jami'ar hukumar ta rabawa manema labarai ta bayyana cewa, abu mafi muhimmanci a duk lokacin da tashin hankali ya barke shi ne kare rayukan fararen hula.

Ta ce yanzu haka hukumarta na aiki kafada da kafada da abokan hulda na cikin gida da na waje da ke kasar, domin sanin adadin fararen hulan da ke bukatar taimako.

Don haka ta yi kira ga dukkan sassan da ke gaba da juna, da su baiwa hukumomin agaji damar isar da kayayyakin tallafi ga fararen hular da ke matukar bukata.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China