in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin mutanen da suka rasu sakamakon babbar gobara a India ya karu zuwa 110
2016-04-11 10:24:53 cri
Wani jami'in kasar India ya bayyana a ran 10 ga wata cewa, adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon babbar gobarar da ta tashi a wani gidan ibada na addinin India dake yankin Kollam na jihar Kerala, ya haddasa mutuwar mutane 110 yayin da wasu 390 suka jikkata. Haka kuma, firaministan kasar Narendra Modi ya kai ziyara a wurin da hadarin ya auku, domin yin bincike da kuma ba da jagora kan aikin ceto.

Jami'in ya kara da cewa, ana ci gaba da gyara wurin da gobarar ta tashi. Ya zuw ayanzu kwai wasu mutanen da ake binne a karkashin gidan ibadar da kangayen wasu gidajen da suka wargaje sakamakon tashin gobarar, lamarin da ya sa, mai iyuwa ne za a sami karin rasuwar mutane.

Rundunar sojan kasar India ta aike da jiragen sama masu saukar ungulu da kuma jiragen ruwan soja zuwa wurin domin samar da taimakon agaji, haka kuma, asibitocin wurare daban daban na kasar sun aike da masu aikin likitanci zuwa wurin domin ba da jinya, sa'an nan a wasu wurare kuma, ana neman al'ummomin kasar da su ba da taimakon jini.

Kaza lika, 'yan sandan kasar sun riga sun fara bincike kan wannan bala'i, inda suka bayyana cewa, akwai wasu da su kai kayayyakin wasan wuta ba bisa doka ba a cikin gidan ibadar. A halin yanzu, 'yan sanda sun riga sun kama mutane biyar wadanda mai yiyuwa ne suke da hannu cikin lamarin din, kuma biyu daga cikinsu sun ji rauni mai tsanani, ana ci gaba da ba su jinya a asibiti a yanzu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China