in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane a kalla 109 ne suka mutu a Indiya sakamakon wani turmitsitsi
2013-10-14 10:56:00 cri

A ranar Lahadi 13 ga wata ne, aka samu wani turmitsitsin jama'a mai tsanani a yankin Datia da ke jihar Madhya ta kasar India, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane a kalla 109, kana wasu mutane fiye da 115 suka ji rauni.

Wannan lamari ya faru ne a rana ta karshe ta bikin ibadar gargajiya ta kasar Indiya wato "Navratri Festival", inda jama'a fiye da dubu 250 daga sauran jihohin kasar suka isa jihar Madhya don halartar bikin. Yayin faruwar hadarin, akwai mutane da yawansu ya kai dubu 50 a wurin Ibadar. Bisa rahotannin da kafofin watsa labarai na wurin suka bayar, an ce, wasu mutane ne suka yi kokarin tsallake jerin gwanon da aka yi, kana suka yada jita-jitar cewa, babbar gadar za ta karye, wannan ya sanya jama'a suka firgita, kuma suka rika taka juna, wasu mutane suka yi tsalle suka fada cikin kogin har suka rasa rayukansu. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China