Kafofin watsa labaru na wurin sun ruwaito bangaren 'yan sanda na cewa, gobara ta tashi da misalin karfe 3 da minti 30 a safiyar ranar, kuma mai yiwuwa ne gobara ta auku sakamakon kayayyakin wasan wuta da aka ajiye a gidan ibadar da za a amfani da su a yayin biki. An ce, kafin haka 'yan sanda sun taba gargadin wannan gidan ibadar game da amfani da kayyakin wasan wuta.
Bisa labarin da aka samu, ya zuwa ranar 10 ga wata da karfe 7 na safe, an riga an samu nasarar kashe gobarar. A yayin lamarin ya faru, akwai mutane dubu 10 zuwa 15 da suke cikin gidan ibada. A yanzu haka ana ta samun rasuwar mutanen da suka jikkata, yawancinsu kuma mata ne da yara kanana. Yanzu an riga an kai masu rauni a asibitoci don samun jinya. Bangaren soja kuma ya aika da jiragen sama masu saukar ungulu domin shiga aikin ceto. (Bilkisu)