Babban bankin Najeriya wato CBN ya sanar a Talatar nan cewar, zai yi amfani da farashi na kashi 11 cikin 100 na kudin ruwa wajen baiwa bankunan kasuwanci rance a kasar.
Gwamnan babban bankin kasar Godwin Emefiele, ya tabbatar da hakan a taron manema labaru game da makomar kwamitin tsara kudaden kasar wato MPC.
Gwamnan babban bankin ya ce, CBN ba shi da wani shiri a yanzu, na rage darajar kudin kasar.
Emefiele, ya shedawa manema labaru cewar, duk da kasancewar a cikin watanni 14 da suka gabata, farashin danyen mai na ci gaba da faduwa a kasuwannin duniya, duk da hakan gwamnatin kasar ba ta da niyyar rage darajar kudinta.
A watan Nuwambar shekarar 2014, an rage darajar kudin kasar da kashi 22 cikin dari, inda aka dinga sayar da Naira daga 155 zuwa 168 a kan kowace dalar Amurka.
CBN ya ce, zai ci gaba da daukar matakan da suka dace ga tsarin kudaden kasar wanda zai dace da farashin da ake sayar da danyen man a kasuwannin duniya.(Ahmad Fagam)