Ministan yada labaru na Najeriyar Lai Muhammad, ya fada a yayin zantawa da manema labarai cewar, game da batun amincewa da kasafin kudin, babu wani sabani tsakanin gwamnati da majalisar dokokin kasar.
Yace maganar da ake yadawa cewar shugaban kasar yayi watsi da kasafin kudin ba gaskiya ba ne.
Minsitan yace bisa ga tsarin kasafin kudi, ana rubuta bayanai na alkaluma da aka amince dasu ne, kafin kuma tsagin majalissar ya gabatar da cikakken kasafin.
Lai ya ce, daga bisani majalisar zata mikawa shugaban kasar kwafi na ainihi bayan an kammala gyare gyare.
A cewar ministan, babu koma baya game da sha'anin kasafin kudin kasar, ya kara da cewar ma'aikatar tsara kasafin kudi tana cigaba da aiki tare da majalisar dokokin domin kammala wannan aiki a kan lokaci. (Ahmad)