An mika Ali Audu da Abdulmumini Abdullahi a hannun rundunar sojojin Najeriya da ke jihar Yobe mai makwabtaka, in ji Shaba Alkali, shugaban 'yan sandan jihar Taraba, kafin ya kara da cewa an cafke kowanansu a ranar 22 ga watan Fabrairu da ranar 5 ga watan Maris.
Mutanen biyu suna cikin takardar jerin sunayen mambobin Boko Haram da ake nema ruwa jallo da rundunar sojojin Najeriya ta fitar a shekarar da ta gabata.
A kalla kamandojin Boko Haram kusan biyar ne rundunar ta cafke a shekarar da ta gabata a wasu yankunan kasar.
Boko Haram ta kashe dubun dubatar jama'a a Najeriya tun farko kaddamar da ayyukanta a shekarar 2009 bisa yunkurinta na kafa kasar musulunci.
Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ta karya lagon wannan kungiya, amma har yanzu mayakanta na cigaba da kai hare hare jehi jehi a wannan kasa da ke yammacin Afrika. (Maman Ada)