Gao Hucheng ya bayyana a gun taro mai taken "lokacin yin kwaskwarima ga G20: cimma burin duniya ta hanyar shirin kasar Sin" na dandalin tattaunawa na Asiya na Bo'ao na shekarar 2016 da aka gudanar a jiya Alhamis, cewa yanzu ana samun raguwar ciniki a duniya, kuma ana bukatar matakin inganta zuba jari a tsakanin kasa da kasa. Don haka kungiyar G20 ke da alhakin daukar matakai don taka muhimmiyar rawa, wajen sa kaimi ga bunkasar harkar zuba jari da cinikayya a duniya.
Haka zalika kuma, Gao Hucheng ya ce, Sin tana fatan kokari tare da bangarori daban daban, don sa kaimi ga kungiyar G20, ta yadda za ta samu kyakkyawan sakamako a fannin tattalin arziki, da cinikayya, don amfanar dukkanin duniya a tsawon lokaci. (Zainab)