Hukumar bunkasa ci gaban tattalin arzikin Afrika ta MDD UNECA, da kungiyar tarayyar Afrika AU, za su gudanar da taro na mako guda game da raya ci gaban Afrika daga ranakun 31 ga watan Maris zuwa 5 ga watan Aprilu a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.
A wata sanarwar da UNECA ta fitar a Larabar da ta gabata ta ce, ana sa ran taron makon na ci gaban Afrika, zai tabo batutuwa ne da suka shafi bakin haure, da ci gaban masana'antu, da tsaron kan iyakoki da batutuwan yarjejeniyar kasa da kasa da suka hada da batun shirin ci gaban karni da dai sauransu.
Sanarwar ta kara da cewar, ana sa ran sama da wakilai dubu 3 ne za su halarci taron, ciki har da shugabannin kasashe, da kwararru a fannin ci gaban masana'antu, da makamashi, da kididdiga, da harkar bankuna, da kuma sauyin yanayi.
Taron na shekara shekara na hadin gwiwa tsakanin UNECA da AU, ana sa ran za'a gudanar da taron ministoci wanda kwararru za su jagorance shi.
Sanarwar ta kara da cewa, taron na ministoci zai kunshi ministocin tattalin azriki da na kudi ne, na mambobin kasashen AU da ministocin kudi da tsare tsaren tattalin arziki na UNECA, inda za su tattauna muhimman batutuwa da suka shafi ci gaban Afrika.(Ahmad Fagam)