in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD da AU sun yi alkawarin inganta dangantaka a bangaren zaman lafiya da tsaro
2014-09-22 10:55:56 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon a ranar Lahadin nan ya gana da shugabar kwamitin tarayyar kasashen Afrika AU Madam Nkosozana Dlamini-Zuma, inda gaba dayansu suka yi alkawarin inganta hadin gwiwa a tsakanin su a bangaren zaman lafiya da tsaro.

A lokacin ganawar tasu, shugabannin biyu sun tattauna dabarun inganta hadin gwiwa tsakanin cibiyoyin biyu, da kuma hanyoyin da za'a ci gaba da bi domin ganin an inganta hadin gwiwa a wadannan bangarorin biyu, in ji kakakin majalissar a bayanin da ya yi wa manema labarai.

Haka kuma a lokacin ganawarsu, Mr. Ban da Madam Zuma sun yi nazarin kalubalen da zaman lafiya da tsaro ke fuskanta a nahiyar ta Afrika, musamman a kasashen Libya, Mali, yankin Sahel, Somaliya, Sudan ta Kudu da yankin babban tabkin Afrika, in ji kakakin majalissar.

Mr. Ban daga bisani ya jaddada aniyar majalissar ta ganin hadin gwiwa da kungiyar ta AU, kuma ya bayyana irin kokarin da majalissar take wajen taimakawa kasashen yammacin nahiyar na ganin sun dakile annobar nan ta Ebola. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China