in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD da AU sun yi kira da a kara kokarin samar da zaman lafiya a CAR
2014-06-03 12:49:53 cri

Jami'ai daga MDD da kuma kungiyar hadin kan Africa AU da kuma kungiyar tattalin arzikin kasashen yankin tsakkiyar Afrika ECCAS, sun kammala wata ziyara tasu ta hadin gwiwa ta kwanaki uku a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya CAR, tare da gabatar da kira a kan karin taimako daga kasashen duniya domin girka zaman lafiya mai dorewa a kasar.

Jami'an wadanda suka hada da wakiliya ta musamman mai kula da harkokin mata, zaman lafiya da tsaro ta kungiyar hadin kan Afrika AU, Bineta Diop, da kuma babbar darekta ta mata ta MDD Phumzile Mlambo-Ngcuka, sun kai wata ziyara ta jan hankali zuwa jamhuriyarr Afrika ta Tsakiya a watan Mayun da ya gabata domin nuna halin da mata da yara suka shiga, da kuma karin bukatar taimako daga kasashen duniya, tare kuma da kara karfafa rawar da mata ke takawa, mata wajen samar da zaman lafiya da sasantawa da samun daidaito da juna a kasar.

Wata sanarwa ta hadin gwiwa mai sa hannun MDD da kungiyar tarayyar hadin kan Afrika AU da kuma kungiyar tattalin arzikin kasashen Afrika ta tsakiya ECCAS, wacce aka bayar a karshen ziyarar tasu, ta ce, rikicin da ake ci gaba da tafkawa a Afirka ta Tsakiya yana da matukar sosa rai, kuma mata da yara da 'yan mata, rikicin ya shafe su sosai.

Sanarwar ta ce, rikicin ya sa mutanen kasar sun shiga cikin wani hali na wahala, kuma dubannin mutane sun sami rauni, wasu kuma sun rasa rayukansu.

Kamar dai yadda sanarwar ta ce, fiye da mutane dubu 554 ne sun rasa muhallansu a sakamakon rikicin. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China