in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta jaddada muhimmancin karfafa dangantaka da AU
2014-12-17 14:36:23 cri

Kwamitin sulhu na MDD ya jaddada muhimmancin karfafa dangantaka tsakanin MDD da tarayyar Afrika (AU) domin taimaka wajen kara karfin magance kalubalolin tsaron da ake fuskanta tare a nahiyar Afrika, in ji wannan hukuma ta MDD a albarkacin wani zaman taron da ake kebe kan dangantaka tsakanin kungiyoyin biyu.

A cikin wata sanarwa da mambobin kwamitin 15 suka amince, kwamitin sulhu ya yi la'akari da nasarorin da aka samu a fannin dangantaka tsakanin MDD da AU. Baya ga karfafa wannan dangantaka, kwamitin ya yi tunanin cewa, akwai muhimmancin da a karfafa dangantaka mai karfi tare da kwamitin wanzar da zaman lafiya na tarayyar Afrika domin hada karfi da karfe, ta yadda wannan kungiya za ta samu karfin magance duk wasu kalubalolin tsaro da ake fuskanta a Afrika.

A cikin wannan sanarwa, kwamitin ya yi imani da taimakon da AU take bayarwa wajen rigakafi da warware rikice rikice a nahiyar Afrika, tare da bayyana goyon bayansa kan ayyukan da kungiyar ta gudanar, da ma wasu ayyukan makamantan haka da kungiyoyin shiyyoyi suke gudanarwa. Haka kuma mambobin kwamitin sun nuna yabo ga taimakon da kungiyar AU ta bayar wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro, musammun ma a yankin Darfur na kasar Sudan, da kasashen Mali, Afrika ta Tsakiya da Somaliya, da kuma kokarin da take game da rundunonin hadin gwiwa na shiyyar Afrika domin karfafa karfinsu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China