Yayin ganawar tasu, Mr Zhang ya ce, Habasha ta kasance abokiya mai muhimmanci ga kasar Sin ta fuskar hadin gwiwa da kasashen Afrika, a cikin shekaru 45 da kafuwar dangantakar diplomasiyya tsakaninsu musamman ma a shekarun nan baya, shugabannin kasashen biyu na zurfafa mu'ammala tsakaninsu .
Sannan kuma inji Mr Zhang bangarorin biyu na samun ci gaba sosai ta fuskar yin hadin kai, hakan ya sa, dangantakar dake tsakaninsu ya zama abin koyi wajen hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa. A don haka Majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na mai da muhimmanci sosai wajen raya dangantakar dake tsakaninta da majalisar wakilan Habasha.
A nasa bangare, Kassa Teklebirhan ya ce, Habasha na mai da kasar Sin matsayin muhimmiyar abokiyar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, kuma tana fatan ci gaba da yin mu'ammala tsakanin manyan shugabannin kasashen biyu tare da tabbatar da matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma da kuma aiwatar da manyan ayyukan hadin gwiwa a tsakaninsu. Sa'an nan a habaka mu'ammala tsakanin jama'arsu da majalisun su.(Amina)