A ranar 31 ga watan Oktoban shekarar 2015 ne, wani jirgin saman fasinjan kasar Rasha kirar Kogalymavia da ya tashi daga Sharm El-Shekih a kan hanyarsa ta zuwa birnin St Petersburg na kasar Rasha, ya fadi jim kadan da tashinsa a zirin Sinai, inda fasinjoji 217 da ma'aikatan 7 dake cikin jirgin suka halaka, akasarinsu 'yan kasar Rasha.
Hukumar tsaron Rasha ta bayyana cewa 'yan ta'adda ne suka harbo jirgin. Bayan aukuwar lamarin, kasashen Rasha, Birtaniya, Faransa, Jamus da sauransu sun sanar da dakatar da zirga-zirgar jiragen samansu zuwa kasar ta Masar, matakin da ya haifar da babbar koma baya game da sha'anin yawon shakatawa na kasar Masar. (Bako)