A cikin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 13, an gabatar da cewa, za a mayar da aikin nazarin sararin samanniya a matsayin daya daga cikin manyan ayyuka guda 6 na muhimman ayyukan nazari da kasar Sin za ta yi game da yin kirkire-kirkire kan harkokin kimiyya da fasaha.
Zhou Jianping ya ce, daga tsakiyar shekarar bana zuwa watanni shidar farkon shekarar badi, Sin za ta gudanar da aikin gwaji kan tashar sararin samaniya game da harba kumbo mai dauke da mutane, don tantance fasahar kafa tashar sararin samaniya a nan gaba.(Bako)