in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin ya yi bayani kan huldar diplomasiyya tsakanin Sin da sauran kasashen duniya
2016-03-08 19:54:51 cri

A safiyar yau Talata ne aka kira taron manema labaru na taron shekara shekara karo na hudu na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na 12, inda ministan harkokin wajen Sin, Wang Yi ya yi bayani kan harkokin da suka fi jawo hankulan duniya, da dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, da dangantakar dake tsakanin Sin da Koriyar ta Arewa da dai sauransu.

A yayin da yake amsa tambayar wani dan jarida dangane da batun tekun kudancin kasar Sin, minista Wang Yi ya bayyana matsayin Sin kan wannan batue, ya ce,

"Tun asali tsibiran Spratly mallakar Sin ne. Kowane Basine na da alhakin kiyaye su. Ba mu taba gabatar da bukatar sabon yankin kasar ba, kuma ba za mu yi haka a nan gaba ba."

Wang Yi ya karyata da rahotannin da ake yayatawa cewa, wai Sin ta jibge sojoji a tekun kudanci, tare da kawo cikas ga zirga zirgar jiragen ruwa a wannan yanki. Ya nanata cewa, kasar Sin ta kafa kayayyakin tsaro a tsibiran ne da nufin kare kanta, kuma 'yanci ne na kare kai kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada. A matsayinta na kasa mafi girma dake dab tekun kudanci, Sin na fatan ba da kariya ga 'yancin zirga zirga a wannan yanki. Kuma bisa kokarin da Sin da sauran kasashen dake wannan yanki suke yi, tekun kudancin Sin ya zama daya daga cikin hanyoyin zirga zirgar jiragen ruwa mafi 'yanci da tsaro a duniya.

Yanzu yanayin da ake ciki a zirin Koriya ya fi jawo hankalin kowa da kowa. Game da wannan batu, Wang Yi ya ce, "Kakaba takunkumin da aka yi wa kasar koriya ta Arewa ya zama dole, yayin da tabbatar da zaman lafiya ya zama abin dake gaban kome, sannan yin shawarwari ya zama hanya mafi dacewa da za ta daidaita wannan batu". Game da tambayar da aka yi na cewa, ko Sin za ta sake taimakawa Koriya ta Arewa domin yaki da kasar Amurka, minista Wang ya amsa cewa,

"Akwai dankon zumunci tsakanin Sin da Koriya ta Arewa. Sin tana dora muhimmanci sosai kan dankon zumunci dake tsakanin kasashen biyu. Idan Koriya ta Arewa na kokarin samun bunkasuwa da tsaro, Sin za ta taimaka mata bisa iyakacin kokarinta. Amma a sa'i daya, ko kadan ba za mu canza matsayinmu game da kawar da makaman nukiliya a zirin Koriya ba. Ba za mu yarda da abin da Koriya ta Arewa ta yi na gudanar da shirin samar da makaman nukilya da makamai masu linzami ba."

Har wa yau, dangantaka tsakanin Sin da Amurka ta jawo hankalin duniya sosai. Game da tambayar da wakilinmu ya yi, minista Wang ya ce,

"A matsayinsu na manyan kasashe, Sin da Amurka suna hadin gwiwa da juna, haka ma akwai gogayya tsakaninsu. Wannan shi ne halin da ake ciki. Game da wannan batu, aikinmu shi ne fuskanta da kuma daidaita matsaloli, da zurfafa hadin gwiwa, tare da kyautata gogayya da bambance-bambancen da ke tsakaninsu, har daga karshe mu canza su zuwa yin hadin gwiwa. A cikin 'yan kwanakin da suka gabata, an samu wasu matsaloli a yankin tekun. Duk da haka, na yi imani cewa, bayan da Amurka ta canja ra'ayinta, za mu duba yadda za mu karfafa hadin gwiwa tsakaninmu dangane da batun yankin tekun na kasar sin. Wannan gogayya ta taso ne bayan da wasu Amurkawa suka nuna tababa ga kasar Sin, inda suke nuna damuwar cewa, ko wata rana Sin za ta maye gurbin Amurka? A nan dole ne in sake jaddada cewa, Sin ba Amurka ba ce, kuma ba za ta canza kanta zuwa kasar Amurka ta daban ba."(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China