in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron shekara-shekara na majalisar CPPCC na 12
2016-03-03 18:59:43 cri

Yau Alhamis 3 ga wata yamma ne, aka bude taron shekara-shekara na bana na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin CPPCC karo na 12 a nan birnin Beijing. A yayin bikin kaddamar da taron, shugaban majalisar Yu Zhengsheng ya gabatar da rahoto kan ayyukan zaunannen kwamitin majalisar, inda ya nuna cewa, a shekarar 2016, aikin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar ta Sin zai himmatu ga ba da shawara kan yadda za a aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 13 a nan kasar Sin, za ta kuma mai da hankali kan gudanar da ayyukanta yadda ya kamata, yayin da za ta karfafa aikinta na sa ido da kuma ba da shawara ga ayyukan gwamnatin kasar, ta yadda majalisar za ta ba da gudummawa yadda ya kamata.

Da karfe uku na yamman yau ne, aka bude taron a babban dakin taron jama'a da ke nan birnin Beijing, wasu shugabannin jam'iyyar kwaminis da na gwamnatin kasar Sin, ciki har da shugaban kasar Xi Jinping da firamista Li Keqiang sun halarci bikin bude taron.

Taron majalisar na CPPCC na shekara-shekara za a kashe kwanaki 11 ne ana yinsa, inda mambobin majalisar sama da dubu biyu za su ba da shawara kan yadda za a aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 13 a nan kasar Sin.

Shekarar 2016 shekara ce da gwamnatin kasar Sin ta fara yin kokarin ganin ta mayar da kasar zama kasa mai matsakaicin karfin tattalin arziki, kuma shekara ce da aka kara zurfafa gyare-gyare kan tsarin tattalin arzikin kasar, kuma a farkon shekara ce za a fara aiwatar da shirin shekaru biyar-byar na 13 na bunkasa kasar Sin. Bisa tunanin da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, wato jam'iyyar siyasa dake rike da ragamar mulkin kasar ta gabatar na kirkiro sabbin hanyoyi da samun daidaito tsakanin sassa daban daban kan yadda za a nemi bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba a yayin da ake ci gaba da bude kofa ga sauran kasashen duniya da cin gajiyar kyakkyawan sakamako tare. A cikin rahoton da ya gabatar, Mr. Yu Zhengsheng ya gabatar da muhimman ayyukan da majalisarsa za ta yi a bana.

"Mambobin majalisar za su fi mai da hankali wajen ba da shawarwarin da za su iya kawo sakamako na a zo a gani kan yadda za a aiwatar da shirin shekaru biyar-biyar na 13 kamar yadda ya kamata, da matakan yin gyare-gyare kan fannonin samar da kayayyaki."

Bugu da kari, Yu Zhengsheng ya jaddada cewa, "Dole ne a kara mai da hankali kan yadda ake aiwatar da muhimman matakan yin gyare-gyare da manufofin da kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin zai gabatar."

Majalisar CPPCC, majalisa ce ta hadin gwiwar al'ummomin kasar Sin, kuma wata muhimmiyar hukuma ce ta fuskar yin hadin gwiwa a tsakanin jam'iyyu da ba da shawara kan harkokin siyasa a karkashin shugabancin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, hakan da ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsarin dimokuradiyya mai sigar gurguzu a harkokin siyasar kasar Sin. A cikin rahoton aiki na bana, an yi cikakken bayani kan yadda majalisar CPPCC za ta kara taka rawa a fannin yin hadin gwiwar al'ummar kasar ta Sin. Yu Zhengsheng ya ce, "Dole ne a girmama hakkokin wadanda ba 'yan jam'iyyar JKS ba a harkokin dimokuradiyya tare da ba su tabbacin samun irin wannan hakki, da inganta tattaunawar da ke tsakanin jam'iyyu da kungiyoyi a al'amuran hukumar CPPCC, da zurfafa hadin gwiwar da ke tsakanin jam'iyyar JKS da kuma wadanda ba mambobin jam'iyyar ba. Har wa yau a kyautata tuntuba da yin cudanya da sassa daban daban na al'ummar kasar, a kokarin kara samar da sharadi mai kyau wajen ba da shawara kan harkokin siyasa da bayyana ra'ayi ko bukata yadda ya kamata, ta mabambantan hanyoyi na ba da shawara kan harkokin siyasa da yin mu'amala. " (Sanusi Chen, Tasallah Yuan, Maryam Yang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China