in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin kasar Sin ta fitar da matakan yadda za ta sauke nauyin dake wuyanta a shekarar 2016
2016-03-05 13:20:43 cri

A safiyar yau 5 ga watan Maris, aka kaddamar da taron shekara-shekara karo na 4 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na 12 a nan birnin Beijing, inda aka fitar da matakan yadda gwamnatin kasar za ta sauke nauyin dake wuyanta a shekarar 2016. Shekarar 2016 shekara ce da ake fara cimma burin raya kasar Sin da ta zama kasa mai matsakaicin karfin tattalin arziki, kuma farkon shekara ce da za a aiwatar da shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa kasar na 13, sannan muhimmiyar shekara ce da ake kwaskwarimar tsarin tattalin arzikin kasar. Sakamakon haka, yadda gwamnatin kasar za ta daidaita matsaloli da kalubaloli iri daban daban dake kasancewa a gabanta a shekarar 2016 yana jawo hankalin kafofin watsa labaru na duniya.

A shekarar 2015, saurin karuwar tattalin arzikin kasar Sin ya kai kashi 6.9 cikin dari kawai, kuma a watan Janairun da ya gabata, yawan darajar kayayyakin da ake fitarwa daga kasar Sin yana ta raguwa, wato yanzu yanayin tattalin arzikin da kasar Sin ke ciki ba shi da kyau. Game da wannan halin da ake ciki, Li Keqiang, firaministan gwamnatin kasar Sin ya nuna cewa, a kullum kasar Sin tana samun ci gaba ko da yake ta kan fuskanci matsaloli iri iri, duk da hakan ba wani abun da zai hana ta samun ci gaba. Li Keqiang ya fadi cewa, "Shekarar bana farkon shekara ce da ake kokarin raya kasar Sin da ta zama kasa mai matsakacin tattalin arziki daga dukkan fannoni, kuma muhimmiyar shekara ce da ake namijin kokarin yin kwaskwarimar tsarin tattalin arzikinta. Idan ana son gudanar da ayyukan gwamnati kamar yadda ake fata, dole ne a tafiyar da manufofin da suke shafar dukkan fannoni ba tare da tangarda ba, kuma dole ne a dauki matakan raya sana'o'i daidai, sannan dole ne a aiwatar da manufofin raya masana'antu bisa hakikanin halin da ake ciki, har ma kuma wajibi ne a dauki matakan yin gyare-gyare da za a iya ganin sakamako na a zo a gani. Daga karshe dai, dole ne a samar da manufofin raya zaman al'umma domin biya bukatun da ake da su. Dadin dadawa, dole ne a samu daidaito tsakanin kokarin samun ci gaba da kokarin daidaita tsarin tattalin arziki, ta yadda za a iya tabbatar da ganin an samu saurin karuwar tattalin arziki kamar yadda aka tabbatar. Bugu da kari, dole ne a gaggauta yin kwaskwarimar sana'o'in dake samar da kayayyakin da ake bukata."

A cikin rahotonsa, Li Keqiang ya bayyana cewa, babban buri na shekarar bana shi ne, ganin saurin tattalin arziki na GDP na kasar Sin zai karu da kashi 6.5 zuwa kashi 7 bisa dari. Li Keqiang ya ce, "Bisa hasashen da aka yi kan bunkasuwar tattalin arzikin kasar, an ce, a shekarar bana, ma'aunin tattalin arzikin GDP na kasar zai karu da kashi 6.5 zuwa kashi 7 bisa dari, kana, wannan buri ya dace da ayyukan raya zamantakewar al'umma mai hannu da shuni a nan kasar Sin, yayin da ciyar da aikin gudanarwar kwaskwarimar tsarin tattalin arzikin kasar gaba, haka kuma, zai taimaka wa kasar wajen kiyaye zaman karko da yin hasashe kan harkokin kasuwanci.

Haka kuma, ana kiyaye zaman karko wajen bunkasa tattalin arziki domin samar da guraben aikin yi da kuma ba da tallafi ga al'ummomin kasar, idan adadin karuwar tattalin arziki zai iya kaiwa kashi 6.5 zuwa kashi 7 bisa dari, za a iya tabbatar da samar da isassun guraben aikin yi a kasar."

Shekarar bana shekara ce ta farko wajen cimma nasarar gina zaman takewar al'umma mai hannu da shuni a nan kasar Sin, cikin rahoton din, Li Keqiang bayyana cewa, za a mai da aikin kawar da talauci a matsayin babban aikinmu na bana.

"A shekarar bana, za a kammala aikin kawar da talauci ga mutanen karkarar kasar sama da miliyan 10, ciki har da mutane sama da miliyan biyu wadanda suka kaura daga gidajensu zuwa wurare na daban, domin cimma wannan buri, gwamnatin kasar ta kara kudin samar da taimako ga talakawa har kashi 43.4 bisa dari.

Kaza lika, ya kamata a gudanar da ayyuka bisa bukatunsu da kuma yadda ya kamata, yayin da ake mai da karin hankali kan yankuna masu fama da talauci a yayin da ake gudanar da manufofin ba da tallafi da kuma kiyaye zaman rayuwar al'ummomin kasar."

A yayin bikin bude taron, baya ga rahoton aikin gwamnatin kasar Sin, an mika wa wakilan jama'a mahalarta taron, daftarin shirin raya kasar Sin na shekaru biyar-biyar karo na 13 don su dudduba. A cikin daftarin shirin, Li Keqiang ya ce, "Za a yi kokarin tabbatar da samun matsakaicin saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar tare da raya masana'antu zuwa babban mataki. Wajibi ne a tabbatar da ganin kirkire-kirkire na ba da jagora wajen raya kasa. Har wa yau a ci gaba da bunkasa birane na sabon salo da kuma raya aikin gona na zamani, a kuma kara azama kan samun daidaito yayin da ake raya birane da yankunan karkara tare. Sa'an nan kuma, a sa kaimi ga jama'ar kasar da su yi zaman rayuwa ba tare da gurbata muhalli ba, a kuma gaggauta kyautata muhallin halittu. Dole ne a zurfafa yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, da kafa sabon tsarin raya kasa. Haka zalika za a rika kara kawo wa jama'ar Sin alheri, a kokarin ganin dukkan jama'ar Sin sun ci gajiyar bunkasuwar kasarsu."

Nan da kwanaki 10 masu zuwa, wakilan jama'ar Sin kusan dubu 3 za su dudduba rahoton aikin gwamnatin a tsanake, wanda za su kada kuri'unsu a kansa a yayin rufe taron. Idan sun amince da shi, za a fara aiwatar da shirin raya kasar Sin na shekaru biyar-biyar karo na 13 bisa wannan rahoton aikin gwamnatin, lamarin da ya kaddamar da muhimman ayyukan kafa kasar Sin mai zaman wadata baki daya. (Sanusi Chen, Tasallah Yuan, Maryam Yang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China