in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan majalisar kasar Sin sun ba da shawara kan tsare-tsaren raya kasar
2016-03-03 13:33:47 cri

Yau Alhamis ne aka bude taron shekara-shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin (kwatankwacin majalisar dattawa a wasu kasashe) a nan birnin Beijing, inda 'yan majalisar suke halartar taron, tare da shawarwarinsu dangane da tsare-tsaren raya tattalin arzikin kasar.

Shekarar da muke ciki ta kasance shekara ta farko da aka fara aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 13 a nan kasar Sin, don haka, kamar yadda kakakin taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Mista Wang Guoqin ya fada, kokarin ba da shawara don kara inganta shirin ya kasance wani muhimmin bangare ga ayyukan 'yan majalisar wadanda ke gudanar da taro yanzu.

A cewar mista Mei Xingbao, wani dan majalisa kuma tsohon shugaban wani kamfanin hada-hadar kudi, ya ce wani babban kalubale da ake fuskanta shi ne kokarin rage yawan samar da wasu kayayyaki wadanda ba a bukatarsu sosai a kasuwar kasar. Ya ce,

"Ra'ayina shi ne mu yi amfani da hukumomin hada-hadar kudi don tallafawa kokarin rage yawan samar da wasu kayayyaki. Don cimma wannan buri za a rufe wasu masana'antu ke nan, amma wadannan masana'antu a wani bangare na daban, sun kafu ne daga bashi na wasu bankuna, da kamfanonin hada-hadar kudi. Don haka yaya za a kai ga warware batun bashin da aka ci? A gani na za a iya mayar da bashin ya zama hannayen jarin masana'antun, wadanda za a iya sayar da su daga bisani."

Ban da aikin samar da kaya, sabon shirin raya kasar Sin ya shafi aikin gona, wanda ya bayyana bukatar kara zamanintar da fasaha a wannan fanni. A nasa bangare, mista Xia Qingyou, dan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, kuma shugaban cibiyar nazarin fasahar halittu ta jami'ar kudu maso yamma ta kasar Sin, ya ce kokarin zamanintar da fasahar aikin gona zai taimakawa kiyaye samari da 'yan mata a kauyuka, maimakon su bar gida su shiga birane, ta yadda za a samu damar raya aikin gona cikin wani dogon lokaci. Ya ce,

"Fasahohin aikin gona na zamani sun shafi yadda za a kula da manyan filayen gonaki, a sa'i guda kuma, a yawaita amfani da injuna, gami da samar da ingantattun kayayyaki masu tambura, wadanda za a iya bambance su a kasuwa, wadanda za su taimakawa karin albashin manoma. A da manoma na tafiya ci rani a birane sakamakon karancin kudi da ake samu a kauyuka. Idan za a iya kara yawan kudin da suke iya samu a kauyuka, to, za su koma gidajensu don bude wasu sana'o'i a can. Idan za mu duba batun nan daga wani bangare na daban, wato yayin da muke magana kan yunkurin zamanintar da fasahar aikin gona, abin da ya fi muhimmanci shi ne ko aikin gona zai iya janyo hankalin matasa? Idan aikin zai iya janyo hankalinsu, to, akwai damar samun nasarar raya aikin gona ke nan."

Ban da aikin gona, aikin amfani da albarkatun itatuwa, shi ma ya kasance cikin batutuwan da 'yan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasar kasar Sin suka tattauna a kai. A nan kasar Sin, fadin filayen itatuwa mallakar wasu gungun mutane ya kai kaso 60 bisa dari, cikin fadin daukacin filayen itatuwan kasar. A wannan bangare, mista Huo Xuexi, dan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa, kuma daya daga cikin shugabannin jam'iyyar CPWDP reshen lardin Sha'an Xi, ya ba da shawarar zurfafa kwaskwarima kan tsarin mallakar filayen itatuwa, don taimakawa kokarin samar da karin itatuwa a kasar. A cewarsa,

"Irin tsarinmu na sanya gungun mutane su mallaki filayen itatuwa bai bayyana ainihin wane ne ke da cikakken ikon mallakar filayen ba. Don daidaita batun, mun kara samar da takardun shaidar mallakar fili ga wasu mutane don tabbatar da hakkinsu, sai dai har yanzu ba a daidaita yanayin da ake ciki sosai ba. Ana kasa babban fili zuwa kananan filaye daban daban, karkashin kulawar mutane daban daban, lamarin da ya kan zama matsala ga manoma wadanda suke zuba jari don dasa itatuwa. Don haka na ba da shawara don daidaita wannan fanni."(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China