in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilan taruka biyu sun gabatar da shawarwarin yaki da talauci a Sin
2016-03-04 11:23:07 cri

Kwanakin baya, hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar da alkaluma da ke nuna cewa, a shekarar 2015, yawan masu fama da talauci da ke kauyukan kasar Sin ya ragu da miliyan 14 da dubu 420 idan aka kwatanta da na shekarar 2014, adadin da ya zarce miliyan 10 da ake tunanin za a rage a ko wace shekara. Amma idan ana son cimma burin kubutar da daukacin masu fama da talauci daga mawuyacin halin da suke ciki ya zuwa shekarar 2020 a kasar ta Sin, ya zama wajibi a rage a kalla miliyan 10 a ko wace shekara, wannan ya sa gwamnatin kasar Sin ta bullo da wani tsarin da zai dace a fannin yaki da talauci.

Mataimakin shugaban hukumar kula da al'adu ta lardin Guizhou kuma mamban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Jiang Gangjie ya bayyana cewa, sabon tsarin samar da taimako ga masu fama da talauci ya bukaci a kyautata matakan da ake gudanarwa. Ya ce, "Da farko dai, a halin da muke ciki yanzu, ba mu gano baki dayan su wane ne ke bukatar taimako, shi ya sa ya zama wajibi a yi bincike game da halin da suke ciki. Ban da haka kuma, abu mafi muhimmanci shi ne ma'aikatan hukumomin gwamnatin da aka tura wuraren dake fama da talauci su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata."

Yayin da ake gudanar da aikin yaki da talauci, batun yadda ake amfani da albarkatun da ake samarwa ga masu bukata shi ne ya fi jawo hankulan mutane, saboda lamari ne mai muhimmanci, kuma yana shafar sakamakon da za a samu.

Babbar jami'ar tsaro ta ma'aikatar sufurin kasar Sin kuma mambar majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Cheng Ping ta bayyana cewa, batun sufuri a aikin yaki da talauci, ya kamata a hada aikin gina hanya da shirin ci gaba a wuri guda, ta yadda za a taimaka wajen ci gaban tattalin arzikin wurin dake fama da talauci ta hanyar kyautata yanayin sufuri. Ta ce, "Ya kamata a kara kyautata harkokin sufuri a wuraren da suke bukatar hakan, kafin a tsai da kudurin zaben wuraren da ke bukatar taimako, ya zama wajibi mu yi bincike da kuma nazari, ta haka za a samu kyakkyawan sakamako."

Domin kara ba da taimako ga masu fama da talauci, gwamnatin kasar Sin tana kara zuba jari a wannan fannin, ban da haka kuma, kamata ya yi a sa kaimi ga kamfanoni masu zaman kansu da 'yan kasuwa da su kara mai da hankali kan aikin zuba jari a wannan fannin.

Sakataren kwamitin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na kauyen Wanggang da ke lardin Guizhou kuma mamban majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Hua Quan yana ganin cewa, ya kamata a kara ba da muhimmanci kan wannan batu. Ya ce, "Ya kamata a ba da jagoranci kan kokarin da ake na ganin kamfanoni masu zaman kansu da 'yan kasuwa sun zuba jari a aikin yaki da talauci, ta yadda za su taimaka wajen ci gaban tattalin arzikin kauyuka, musamman a fannonin jari da bayanai da sauransu, misali, idan suka kafa kamfanoni a kauyuka, manoma za su kubutar da kansu daga talauci ta hanyar yin aiki a kamfanonin."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China