Da yake gabatar da jawabi a yayin babban taron majalisar sarakunan kasar na shekarar bana, Zuma ya ce har yanzu akwai bukatar shugabannin al'umma a kasar su zage damtse wajen yakar mugguwar dabi'ar nan da nuna kyama da wariyar launin fata a tsakanin al'ummar kasar.
Shugaba Zuma ya buga misali dangane da wata tarzoma da ta barke a lokacin da wasu fararen fata suka furta kalaman batanci ga bakake, inda suka danganta su da biri a lokacin bikin sabuwar shekara.
Ya kara da cewar, shekaru 22 ke nan da samun 'yanci, don haka ya jaddada cewar kasar Afrika ta Kudu a shirye take ta ci gaba da yakar dabi'ar nuna wariyar launin fata, hakan ne ma yasa gwamnatin kasar ta ayyana watan Mayun shekarar 2016 a matsayin watan isar da sakonnin yaki da nuna wariyar launin fata a kasar.
Zuma ya bukaci sarakunan gargajiyar da su shiga cikin shirin yaki da nuna wariyar, ciki har da bikin tunawa da yaki da nuna wariyar launin fata, da 'yancin dan adam wanda za'a gudanar a ranar 21 ga wannan wata a Durban dake lardin KwaZulu-Natal.(Ahmad Fagam)