A jiya Alhamis ne kasar Afirka ta Kudu ta kammala kulla yarjejeniyar cinikayya da kasar Amurka, matakin da ya baiwa kasar damar cin gajiyar dokar yarjejeniyar cinikayya ko AGOA a takaice na wasu shekaru 10 masu zuwa.
Ministan cinikayya da masana'antu na kasar Afirka ta Kudu Rob Davies wanda ya bayyana hakan a birnin Cape Town ya ce, koda a ranar Jumma'ar da ta gabata ma an shigo da wasu kafafun kaji birnin Durban daga kasar ta Amurka kana daga bisani aka shigar da su kasuwannin kasar bayan da jami'an lafiya da ke aiki a tashar jiragen ruwan kasar suka tantance lafiyarsu.
A baya dai kasar ta Afirka ta Kudu ta hana shigo da kaji daga kasar Amurka sakamakon barkewar cutar murar tsuntsaye a wasu sassan kasar Amurka don gudun yaduwar cutar a cikin kasar.
Shugaba Obama na Amurka ya sanya wa'adin shekarar da ta gabata, inda ya yi barazanar dakatar da kayayyakin amfanin gonan kasar Afirka ta Kudu daga cin gajiyar shirin na AGOA, muddin aka hana shigo da naman kajin Amurka cikin kasar kafin ranar 15 ga watan Maris.
A zantawarsa da ministan cinikayya da masana'antu na kasar Afirka ta Kudu, wakilin Amurka mai kula da harkokin cinikayya Jakada Micheal Froman ya bayyana cewa, zai shaidawa shugaba Obama da ya dage batun barazanar dakatar da kayayyakin amfanin gonan kasar Afirka ta Kudu daga cin gajiyar dokar ta AGOA.
Dokar AGOA dai wata yarjejeniyar cinikayya ce da ke baiwa sassan kasar Afirka ta Kudu da dama cin gajiyar wasu damammaki a kasuwannin Amurka.(Ibrahim)