Jam'iyyar ANC mai mulki a kasar Afirka ta kudu ta yi kiran da a kawo karshen tashin hankalin da ke da nasaba da nuna wariyar launin fata da ya barke jiya Talata a jami'o'in kasar da dama.
Mai magana da yawun jam'iyyar na kasa Zizi Kodwa wanda ya samar da hakan, ya ce, abin takaici ne yadda dangantaka tsakanin al'ummomin kasar ke tabarbarewa, musamman tashin hankalin da ya barke a jami'o'in da ke Free State da kuma Pretoria.
A ranar Litinin ne fada ya barke a jami'ar Free State lokacin da wasu dalibai farar fata suka kaiwa wasu dalibai bakar fata da wasu ma'aikatan jami'ar hari a yayin da suka yi kokarin dakatar da wasan kwallon zari-ruga. Tun a ranar Alhamis din da ta gabata ne ma'aikatan jami'ar ke kokarin kwantar da wutar tashin hankalin.
Tashin hankalin na jiya Talata na zuwa ne bayan fadan da ya barke tsakanin wasu kungiyoyi sakamakon bambancin tsarin harshe da ka'idojin daukar aiki a wadannan jami'o'i
A halin da ake ciki, ana zaman dar-dar a jami'ar Pretoria, tun bayan da fada ya barke tsakanin dalibai da 'yan sanda a ranar Litinin.
Rahotannin na cewa, an kama dalibai da dama. Sai dai dalibai bakar fata suna adawa da yadda ake amfani da harshen Afirkana wajen koyarwa, amma takwarorinsu fararen fata na son su kare yare da al'adunsu a cikin harabar jami'ar.(Ibrahim)