Daya daga cikin mafi tsananin kalubalen dake fuskantar tatalin arzikin kasar Afrika ta kudu shi ne hana saukan shi kasa zuwa wani mataki da sai an sake neman zuba jari, in ji minista a ofishin shugaban kasar Jeff Radebe.
Da yake magana a wajen taron Bloomberg na 'yan kasuwa da tattalin arzikin Afirka da ake yi a birnin Cape Town, wanda yake zuwa a lokacin da kasar ke fuskantar yiwuwar kara samun koma baya a kididdigar da hukumomin kididdiga na duniya kan yi.
Bayan koma bayan da kidididigar cibiyar Fitch, standard and poor, ta yi a bara, matsayin kudin bashin kasar ya kai matsayin kididdiga na BBB da Baa3, abin da ke nufin kasar na gab da shiga cikin jerin kasashen da ba su da tabbaci kuma zai zama hadari wajen zuba musu jari.
Mr Redebe ya ce, gwamnatin kasar na daukan matakai domin tunkarar wannan matsala da cibiyoyin kididdiga ke fargaban faruwan shi
Daya daga cikin ayyukan da gwamnatin Afrika ta kudun take son yi shi ne daidaita bashin ta, kuma ba za ta kara matakin ba da bashin ta ba kuma za ta yi amfani da gwargwadon albarkatun da take da shi, tana mai kira ga 'yan kasar da su tattali wajen amfani da kayayyakin al'umma domin su samar da daraja ga kowace takardar kudin rand da suka kasha, in ji Mr Radebe
Samun jawo hankalin wadatattun masu zuba jari daga kasashen wajen ya kasance wani babban kalubale in ji shi.
Don tunkarar wannan kalubale, ya ce, gwamnati tana kafa wata cibiyar sayayya da za ta zama kamar wajen kula da duk kalubalen da yawancin masu son zuba jari kan fuskanta a bangarori daban daban, da kuma dokoki da dama da za su bi.
Ministan na ofisnin shugaban kasar Jeff Radebe daga nan sai ya yi bayanin cewar, wannan shirin na da niyyar nuna cewar kasar Afrika ta kudun da gaske take yi wajen bude kofofin ta ga masu son zuba jari.(Fatimah)