in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu na MDD zai kada kuri'a game da batun nukiliyar Koriya
2016-03-02 10:49:09 cri
A ranar Larabar nan kwamitin sulhu na MDD zai kada kuri'a game da batun yarjejeniyar gwajin makaman Nukiliyar Koriya ta arewa, bayan da Koriyar ta gudanar da gwajin makamanta karo na 4 a watan Janairu.

Da farko MDD ta shirya gudanar da taron ne da yammacin ranar Talatar data gabata, amma daga bisani ta dage, saboda bukatar da Rasha ta gabatar na neman karin sao'I 24, domin yin nazari kan rubutattun bayanan da suka shafi batun.

A yanzu haka, an shirya gudanar da taron ne da misalin karfe 10 na safiyar ranar Laraba na wurin, wanda yayi dai dai da 1500 agogon GMT.

Amurka ce dai ta gabatar da kudurin a gaban kwamitin mai wakilan kasashen duniya 15 a makon jiya. Kuma kudurin na bukatar a sanya sabon takunkumin dakatar da shirin makamin nukiliyar Koriya ta arewan.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China