in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Kenya ya mika sakon taya murnar sabuwar shekara ga al'ummar Sinawa
2016-02-05 09:41:24 cri
Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta a jiya Alhamis ya aike da sakon taya murnar shiga sabuwar shekarar jama'ar kasar Sin, kuma ya jaddada aniyar karfafa dankon zumuncin dake tsakanin kasarsa da Sin.

Ya ce a madadinsa da iyalinsa yana mika sakon fatan alheri ga al'ummar kasar Sin, yayin da suke bikin murnar shiga sabuwar shekara a Litinin mai zuwa wato 8 ga watan Fabrairun shekarar 2016.

Ya jaddada cewar dangantakar Sino-Kenya ta shafe shekaru sama da 15, kuma tana nan daram, sannan kasashen biyu na cin moriya.

Mista Kenyatta ya kara da cewa, kasashen Kenya da Sin sun kulla dangantakar kasuwanci tun shekaru aruaru da suka shude. Kuma kasashen biyu suna da alaka ta kut da kut ta fuskar yakar cin zali da mulkin mallaka. A cikin wadannan kwanaki, kasahen na yin hadin gwiwa ne wajen bunkasa ci gaba, da yin aiki tare kan muhimman al'amurran ci gaba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China