in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kenya na kokarin yaki da kungiyar Al-Shabaab
2016-01-02 13:17:28 cri
A shekarar 2015, kasar Kenya dake gabashin nahiyar Afirka ta samu ci gaban tattalin arziki cikin sauri, da tabbatar da zaman lafiya a fannin siyasa, haka kuma ta kara daukar tsauraran matakai a wajen yaki da kungiyar Al-Shabaab.

A kwanan baya, ministan harkokin cikin gida na kasar ta Kenya, Joseph Nkaissery ya bayyana cewa, a bara, sakamakon cin gajiyar karuwar karfin yaki da ta'addanci, da amfani da sabbin fasahohi, 'yan sandan Kenya sun murkushe makarkashiyar kungiyar Al-Shabaab ta kai harin ta'addanci a kasar sau da dama. Bayan haka, an ba da labarin cewa, sojojin tsaro na Kenya na kokarin cafke 'yan kungiyar Al-Shabaab dake boye a iyakar kasa tsakanin Kenya da Somaliya.

Masana suna ganin cewa, an riga an sami bambancin ra'ayi a kungiyar, shi ya sa karfinta na tsara kai harin ta'addanci ya ragu. Hakan zai ba da taimako ga Kenya wajen murkushe kungiyar, domin tabbatar da zaman lafiya a kasar.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China