Ministan tsaron kasar Rasha Sergei Shoigu a Talatar nan ya sanar da cewar, kasar ta kai farmaki ma sansanonin kungiyar IS a kasar Syria da makamai masu linzami kirar Kalibr daga cikin jiragen ruwanta da ta jigbe a Bahar Rum.
A cewar Shoigu, harbin makaman masu linzami daga jiragen ruwan na yaki an samu nasarar aiwatar da manyan hari a dai dai kan sansanonin kungiyar guda biyu.
Wannan shi ne karo na farko da sojojin yaki na ruwan mai suna Rostov-on-Don suka yi amfani da makami mai linzamin na Kalibr, in ji Shoigu kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar Tass ta ruwaito shi yana bayani a ganawar da ya yi da Shugaba Vladamir Putin.
Makasudin manyan harin shi ne a kan sansanonin kungiyar'yan ta'addan dake gundumar Raqqa a kasar Syria, kuma ya ce suna da imanin cewa, harin ya kawo babbar illa ga wajen adana makaman kungiyar da masana'antar ma'addinanta da ma ababen da suka shafi man da suke da shi.
A bayanin da ya yi, har illa yau Rasha ta sanar wa Isra'ila da Amurka da niyyarta ta kai wannan hari a kan sansanonin'yan ta'addan ta hanyar amfani da makamai masu linzami daga jiragen ruwan yakinta.(Fatimah Jibril)