A yayin ziyarar aiki da ya yi a babban birnin Cote d'Ivoire, shugaba Yayi Boni ya bayyana cewa, "hakika, muna shirin hada karfi domin yaki da ta'addanci. A bangaren kungiyar ECOWAS, za mu hada kokarin mu tare."
A nasa ra'ayi, shugaban Cote d'Ivoire Alassane Ouattara, ya bayyana cewa dole a samu tuntubar juna tsakanin shugabanni, ta yadda za a samu karfin fuskantar wannan matsala. A ganinsa, kada a nuna sassauci wajen yaki da wannan annoba, kamata ya yi a ba da shawarar karfafa ayyukan hada karfi da karfe.
Shugaban na Cote d'Ivoire da takwaransa na Benin sun yi kuma allawadai da hare-haren ta'addancin baya bayan nan a Burkina Faso da suka halaka mutane 30 da jikkata wasu dama.
Watanni biyu da suka gabata, a cikin watan Nuwamban, wani harin ta'addanci a birnin Bamako na kasar Mali ya halaka a kalla mutane 27. (Maman Ada)