in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Amurka da Rasha sun tattauana kan batutuwan Ukraine, Syria da kuma DPRK
2016-01-14 09:58:29 cri

A jiya ne shugaba Barack Obama na Amurka ya zanta da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, ta wayar tarho kan wasu batutuwan kasa da kasa.

Batutuwan da shugabannin biyu suka tattauna sun hada da rikicin kasar Ukraine, da shirin tattauanawar zaman lafiya na kasar Syria, da kuma gwajin makamin nukiliya na baya-bayan da kasar Koriya ta Arewa ta yi.

Bugu da kari, shugaba Obama ya jaddada muhimmancin amfani da hanyar diflomasiya wajen warware rikicin kasar Ukraine ta hanyar aiwatar da yarjejeniyar Minsk da dukkan bangarorin biyu suka rattabawa hannu.

A dangane da batun Syria kuwa, shugabannin biyu sun bukaci da a hanzarta aiwatar da kudurin da kwamitin sulhu na MDD ya amince da shi game da rikicin kasar ta Syria. Sai dai shugaban biyu sun amince da a kara daukar matakan da suka dace na ganin an tattauna tsakanin wakilan 'yan adawar kasar da gwamnatin kasar karkashin kulawar MDD a kokarin da ake na rage kaifin rikicin kasar da kuma yanayin jin kai da al'ummar kasar ke ciki.

Daga karshe Obama da Putin sun tattauna muhimmancin hadin gwiwar kasa da kasa don mayar da martani game da gwajin makamin nukiliyar da kasar Koriya ta Arewan ta yi.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China