in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta kara kakabawa Rasha takunkunmi saboda rawar da take takawa a rikicin Ukraine
2014-07-17 10:51:15 cri

Amurka ta kakabawa wasu bankuna na kasar Rasha da kuma kamfanoni na makamashi da tsaro na Rasha takunkumi saboda rawar da kasar ke takawa a rikicin Ukraine.

Jaridar New York Times, ta bayyana a cikin shafinta na internet cewar, kamfanonin da aka kakabawa takunkumin sun hada da babban kamfanin albarkatun man fetur na Rasha Rosneft, da kuma bankin Gazprombank, da wasu bankunan guda biyu da kuma wasu manyan kamfanonin samar da iskan gas guda biyu.

Kakakin fadar gwamnatin Amurka Mr. Josh Earnest ya ce, sabbin takunkumin sun kasance mataki mafi tsauri da Amurka ta dauka a kan Rasha, kuma hakan zai haramtawa kamfanonin Rasha shiga wasu kasuwanni na Amurka, saboda har yanzu Rasha ta kasa daukar matakai na dakusar da rikicin na Ukraine. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China