in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta ce bai dace Rasha da gayyaci 'yan adawan Syria a tattaunawar mako mai zuwa ba
2015-11-04 10:08:27 cri

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta bayyana cewa, bai kamata Rasha ta gayyaci bangaren adawar Sham a tattaunawar da za a yi a Rashan ba.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka Elizabeth Trudeau ta shaidawa manema labarai cewa, kamata ya yi Rasha ta mayar da hankali kan mayakan ISIL, sannan ta yi amfani da matsayinta a Syria ta yadda za a zabi gwamnatin da jama'a za su amince da ita.

Madam Trudeau ta kara da cewa, akwai lokaci da kuma wurin da ya dace a gayyaci kungiyoyin adawar kasar ta Syria, don haka, ba a kai ga wannan mataki ba tukuna.

Jami'ar ta ce, a yanzu kamata ya yi kasashen da batun sasanta rikicin kasar ta Syria ya shafa su mayar da hankali kan yarjejeniyar da aka cimma a taron Vienna.

Bayanai na nuna cewa, taron da kasashen duniya suka gudanar game da kasar ta Syria a ranar Jumma'ar da ta gabata, bai kai ga cimma tartibin yarjejeniya game da makomar shugaba Bashar al-Assad ba, ko da yake bakin wasu masu fada a ji a tattaunawar ya zo daya game da yadda za a warware matsalar kasar da yaki ya wargaza.

Sai dai ministocin harkokin wajen kasashen Rasha da Amurka sun shaida wa taron manema labarai na hadin gwiwa cewa, suna da bambancin ra'ayi kan makomar shugaba Assad, amma wannan ba zai hana kokarin da ake na kawo karshen yakin da ake yi a kasar ba.

Amurka dai ta soki yadda Rasha take kai hare-hare ta sama kan masu adawa da shugaba Assad maimakon mayakan IS.

A mako mai zuwa ne kasar Rasha za ta shirya wata ganawa da jami'an gwamnatin Syria da kuma 'yan adawar kasar, taron da Amurka ke adawa da shi.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China