Hukumar Pentagone ta sanar a ranar Talata da rattaba hannu tsakanin Amurka da Rasha kan wata yarjejeniya da ta shafi tsaro kan ayyukan soja a sararin saman Syria, a yayin da kasashen biyu, ko wace ke kai hare hare ta sama a wannan kasa.
Manyan jami'an ma'aikatar tsaron Amurka da ma'aikatar tsaron Rasha sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar da ta shafi matakan da za a aiwatar domin kaucewa hadura tsakanin jiragen yaki na kawancen da Amurka ke jagoranta da jiragen yaki na Rasha a sararin saman Syria, in ji kakakin Pentagone, Peter Cook, a yayin wani taron manema labarai a birnin Washington. (Maman Ada)