Ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta ce, yanzu haka ministocin harkokin waje, da na tsaron kasar, na shirin ganawa da takwarorinsu na kasar Rasha a ranar Juma'a mai zuwa, da nufin tattauna muhimman batutuwan da suka shafi bukatar warware banbance banbance dake tsakanin bangarorin biyu, ciki hadda rashin yarda da matsaya guda, don gane da matakin da Rasha ta dauka kan mai tonon asirin Amurkan nan Edward Snowden.
Har ila yau, ana fatan zaman da ministocin za su yi, zai nazarci wasu al'amura da suka shafi hadin gwiwar sassan biyu, don gane da huldodin kasa da kasa, da huldar diplomasiyyar siyasa da aikin soji. A cewar kakakin ma'aikatar Jen Psaki, ana sa ran gudanar da tattaunawar da bagarorin biyu suka taba aiwatar da makamanciyarta a shekarar 2007 ne a birnin Washington na kasar Amurka, inda a wannan karo sakataren wajen Amurka John Kerry, da sakataren tsaro Chuck Hagel za su wakilci kasar Amurka yayin ganawar.
Psaki ta tabbatarwa manema labaru cewa, akwai tarin banbance banbance dake tsakanin Amurka da Rasha, tana kuma fatan Rasha za ta yi duba na tsanaki kan muhimman batutuwan da za a tattauna.
Sai dai a yayin da Amurka ke fatan ganin an kawo karshen takaddamar dake tsakaninta da Rasha don gane da sabanin dake tsakaninsu, ciki hadda batun baiwa Snowden mafaka da Rashan ta yi, a hannu guda mataimakin ministan wajen kasar ta Rasha Sergei Ryabkov ya ce, babu wata shawara da Rashan za ta yi don gane da wannan batu.(Saminu)