in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Larabawa za su hada kai don tinkarar kasar Iran
2016-01-11 13:38:45 cri

A jiya Lahadi ne, kungiyar kasashen Larabawa wato AL ta kira taron gaggawa na ministocin harkokin wajenta a hedkwatarta dake Alkahira na kasar Masar, don tattauna harin da aka kai a ofishin jakadancin kasar Saudiya dake Iran.

Bayan tattaunawar, kuma ban da kasar Lebanon dukkan mahalarta taron sun zartas da wani kuduri, inda aka bukaci kasar Iran da ta dauki alhakin lamarin da ya faru kamar yadda yarjejeniyoyin kasa da kasa suka tanada. Sun kuma la'anci kasar ta Iran bisa furta maganganun tayar da hankali da kuma tsoma baki a tsarin shari'a na kasar Saudiya. Bugu da kari, taron ya jaddada cewa, kasashen Larabawa za su hada kai don tinkarar ayyukan nuna gaba da tsokana da Iran ke aikatawa.

Ministan harkokin wajen kasar Saudiya Adel Bin Ahmed Al-Jubeir ya bayyana a wannan rana cewa, idan kasar Iran ba ta dauki hakikanan matakai don kyautata dangantakar dake tsakaninta da kasashen Larabawa dake makwabtaka da ita ba, to kasarsa za ta yi la'akari da kara daukar matakai baya ga yanke huldar diplomasiyya a tsakaninsu.

"Kasar Saudiya ta yanke huldar diplomasiyya a tsakaninta da Iran, ta kuma dakatar da harkokin cinikayya da kuma zirga-zirgar jiragen sama a tsakanin bangarorin biyu, Sannan ta umarci 'yan kasarta da kada su ziyarci kasar Iran, amma wadannan matakai ne na farko da kasar ta Saudiya ta dauka. Yanzu haka muna tunanin tattaunawa tare da sauran abokanmu Larabawa, domin daukar matakai na gaba idan har Iran ta ci gaba da gudanar da ayyukan nuna gaba.

A yayin jawabinsa a taron, ministocin harkokin wajen kungiyar kasashen Larabawa sun nuna goyon baya ga kasar Saudiya. Ministan harkokin wajen kasar Masar Sameh Shukri ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Iran ta haifar da kalubale ga kasar Saudiya sakamakon manyan laifufukan da suka faru a cikin kasar ta Saudiya, wannan kutse ne mai tsanani ta yi wa Saudiya, saboda haka kasar Masar ta nuna adawa sosai a kai.

Bayan haka kuma, kudurin da aka zartas a gun taron, ya la'anci kasar Iran da tsoma baki a harkokin cikin gida na kasashen Syria, Yemen, Bahrain, Lebanon da dai sauransu, lamarin da ya haifar da rashin zaman lafiya a yankin. Game da batun, ministan harkokin wajen hadaddiyar daular Larabawa Abdullah Bin Zayed Al Nahyan yana mai cewa, kasar Iran ta yi amfani da rikicin addinai da nufin mamaye yankin.

"Yanzu haka ya fito fili yadda kasar Iran ta ke tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashen Larabawa, inda a kullum ta ke kokarin tayar da rikicin addini, tana kuma mai da hakan a matsayin hanyar neman mallake yankin. Kasar Iran ta kan kawo matsala, da hanyar samar da kudi ga masu tsattsauran ra'ayi, da horar da 'yan ta'adda da samar musu makamai, da kuma kafa sojojin fararen hula, ta yadda za ta rika tayar da rikici da tashe-tashen hankula, tare kuma da kawo barazanar tsaro a yankin."

A nasa bangaren, babban sakataren kungiyar AL Nabil Elaraby ya bayyana a yayin taron cewa, dole ne kasashen Larabawa su hada kai don hana kasar Iran yiwa harkokin cikin gidan kasashen katsa landa.

"Yada ra'ayin nuna gaba tsakanin addinai, da harkuza rikicin addini tsakanin jama'ar kasashen Larabawa, tsoma baki ne a harkokin cikin gida na duniyar Larabawa, kuma sun haifar da illa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasashen Larabawa. Dole ne kasashen Larabawa su hada kansu, domin hana kasar Iran ta shiga harkokin cikin gidan duniyar kasashen Larabawa ta kowa ce irin hanya."

Bayan haka kuma, bangarori daban daban masu halartar taron sun bukaci babban sakataren kungiyar hada kan kasashen Larabawa ta AL da ya mika wannan kudurin da suka zartas ga kwamitin sulhu na MDD, kana ya bukaci kwamitin sulhun da ya dauki matakan da suka dace kan wannan lamarin. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China