Masu shirya wannan tattaunawar sun bayyana cewa babu wani wakilin gwamnatin Burundi da ya zo.
Amma duk da haka, wasu shugabannin 'yan adawa da 'yan majalisar dokokin Burundi sun halarci shawarwarin.
Augustine Mahiga, ministar harkokin wajen Tanzaniya ta bayyana cewa shirin na da manufar kawo karshen rikicin siyasa dake tarnaki yau da kusan watanni a wannan kasa da ke gabashin Afrika, kuma za a a cigaba da shi yadda ya kamata duk da wasu matsalolin da ake fuskanta.
Wadannan shawarwari na gudana a karkashin kasar Tanzaniya, a matsayinta ta shugabar kungiyar CAE a wannan karo, da kasar Angola dake shugabantar taron kasa da kasa na shiyyar manyan tabkuna (CIRGL) da kuma kasar Uganda da aka dora ma nauyin mai shiga tsakani tun cikin watan Junin da ya gabata domin tabbatar da shawarwari tsakanin bangarorin masu gaba da juna da rikicin Burundi ya shafa.
Sakatare janar na kungiyar CAE, janar Richard Sezibera, ya bayyana cewa kungiyar shiyyar na fatan kawo zaman lafiya a Burundi, inda ya kara da cewa za a yi iyakacin kokari domin tabbatar da wannan tattaunawa da shugaban Uganda Yoweri Museveni ya taimaka wajen shiryawa ganin ta samar da sakamako mai kyau. (Maman Ada)