in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta taya kasashen yammacin Afrika murnar cimma nasarar shawo kan cutar Ebola
2015-12-30 19:34:52 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya bayyana a taron manema labaru da ya gudana a Alhamis din nan cewa, hukumar lafiya ta duniya WHO, ta sanar da shawo kan matsalar yaduwar cutar Ebola a kasar Guinea, tare da bayyana hakan a matsayin babbar nasara da aka cimma wajen yaki da cutar Ebola a yankin yammacin Afrika, matakin da kuma kasar Sin ta yi matukar farin ciki da shi.

A jiya Laraba ne WHO ta sanar da shawo kan cutar Ebola a kasar Guinea. Game da hakan, Mr. Lu Kang ya ce tun bullar cutar Ebola a yankin yammacin Afrika a shekarar bara, kasar Sin ta cika alkawarin da ta dauka na ba da taimakon gaggawa ga kasashen da annobar ta shafa, inda ya zuwa yanzu, ta samar da taimako sau da dama ga wadannan kasashe.

Ya ce yawan likitoci da kwararru da Sin ta tura, ya kai fiye da mutum dubu daya, kuma yawan likitocin yankin da ta horar, ya kai fiye da mutum dubu 10, wanda hakan ya zamo babbar gundumawa wajen shawo kan yaduwar cutar.

A halin yanzu, kasashen da abin ya shafa suna dukufa wajen sake raya tsarin zamantakewar al'ummominsu bayan kawo karshen cutar ta Ebola. A nata bangare kuma, kasar Sin ta sha alwashin gudanar da manufofin da aka tsara, a gun taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afrika da ya gudana a Johannesburg, domin taimakawa wadannan kasashe wajen farfado da tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar jama'a, da inganta tsarin kiwon lafiyar su, ta yadda za a kauce wa sake faruwar irin wannan annoba. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China