in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taron ci gaban kasa da aikin gyare-gyare a birnin Beijing
2015-12-23 12:35:01 cri

A jiya Talata 22 ga watan nan na Disamba ne, aka gudanar da taron ci gaban kasa da aikin gyare-gyare a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda aka tattauna game da matakan da za a dauka don tabbatar da ci gaban tattalin arzikin kasar.

A yayin taron da ya gudana a jiya Talata, mista Xu Shaoshi, darektan kwamitin tsara matakan gyare-gyare da ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, ya ce akwai yanayi mai kyau ga aikin raya tattalin arziki a kasar, ganin yadda ake ci gaba da kokarin gudanar da gyare-gyare ga tsarin tattalin arziki, da rage gibin dake tsakanin shiyyoyin kasar, da sauya tsare-tsaren masana'antu, gami da kokarin aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar masu zuwa.

Duk da haka a cewarsa, za a fuskanci mawuyacin hali a wasu bangarori, ya ce, "A wani bangare, tattalin arzikin duniya bai samu damar farfadowa sosai ba, ta la'akari da rashin karuwar yawan cinikayyar da ake yi, da kuma shirin kara yawan ruwan bashi a baitulmalin kasar Amurka, yayin da kuma farashin manyan kayayyakin ciniki kamar danyen mai ke faduwa. Wadannan abubuwa sun kara nuna cewa sabanin da ake yi a fagen siyasar duniya, da tashin hankalin da ake samu a wasu kasashe, dukkansu sun yi tasiri kan tattalin arzikin Sin ta hanyoyin darajar musayar kudi, da zuba jari, da cinikayya, da dai sauransu. A dayan bangare kuma, wasu manyan kamfanonin kasar Sin ba su son zuba jari domin kaucewa fuskantar hadari, yayin da kananan masana'antu ke fuskantar matsala a fannin neman samun jarin da za a zuba musu."

Dangane da wadannan matsalolin da ya zayyana, mista Xu ya ce, za a dauki matakan da suka dace, da la'akari da yanayin tattalin arziki na yanzu, don tabbatar da samun nasara a wasu manyan ayyuka guda 8, musamman ma a fannin kiyaye karuwar tattalin arzikin kasar Sin.

Matakin da aka dauka, in ji mista Xu, ya hada da wasu manyan ayyukan gine-gine, wadanda suka riga suka janyo jarin da yawansa ya kai kimanin Yuan RMB biliyan 4700. Sa'an nan a nan gaba za a kara mai da hankali kan gudanar da ayyukan gini a wasu wuraren dake da matukar bukata, a cewar Xu, "Za a yi kokarin daukar matakan yaki da talauci don fitar da al'ummar kasar da dama daga kangin talauci, da yin kwaskwarima ga gidaje marasa inganci, da gyaran fuska game da cudanyar layukan wutar lantarki, da manyan ayyukan ban ruwa, da kara shimfida layukan dogo, da kokarin tace ruwan da aka gurbata a wasu wurare, da dai makamantansu."

A cewar jami'i mai kula da tsarin tattalin arzikin kasar Sin, za a dora muhimmanci kan kokarin gyaran fuska ga tsarin samar da kayayyaki a kasar Sin. Aikin da zai shafi ayyuka a fannoni guda 5, wato rage fitar da kayyayaki, da rage kayayyakin da aka ajiye, da rage bin bashi, da rage kudin da ake bukatar kashewa domin samar da kaya, gami da kokarin kyautata wasu fannonin da ba su samu ci gaba sosai ba tukuna. Jami'in ya kara da bayyana cewa, matakan da za a dauka za su kunshi kula da masana'antun dake fuskantar matsala, da rage kudin da gwamnati take karba wajen tallafawa kamfanoni, gami da rage yawan gidajen da ba a sayar da su ba. "Za a tsara shirin baiwa mazauna kauyuka miliyan 100 damar zama a birane, da kokarin biyan bukatunsu na samun gidaje."

Sauran ayyukan da za a yi za su shafi taimakawa jama'a bude kamfanoni masu zaman kansu, da zurfafa gyare-gyare kan tsarin tattalin arziki, da rage gibin dake tsakanin kauyuka da garuruwa, da dai sauransu. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China