Jirgin na kokarin isa tashar ruwan bahar ahmar a birnin Al-makha lokacin da ya kife saboda rashin kyaun yanayi, in ji kamfanin dillancin labaran kasar Yemen SABA, ba tare da bayyana dai dai lokacin da hadarin ya auku ba.
A cikin wata sanarwar da aka buga a shafin internet din ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Yemen, an ce daukacin bakin haure su 70 dake cikin jirgin babu wanda ya tsira kuma dukkan su daga kasar Habasha ne.
Wani jami'in tsaro wanda ya nemi a sakaya sunan shi ya shaida ma kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa jami'an tsaron bakin ruwan na yemen suka gano bakin hauren a ranar lahadi bayan da jirginsu ya kife da tsakar ranar asabar. An baza ma'aikatan ceto da neman wadanda suka saura da rai sai dai ba'a yi sa'a ba don gaba dayan su sun mutu in ji shi.
Yanzu haka jami'an tsaro sun bazama farautar mai jirgin wanda ake kyautata zaton mai safaran mutane ne ba bisa doka ba in ji SABA.