in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Liberiya ta zama mambar kungiyar WTO
2015-12-17 10:27:32 cri
Taron Ministoci karo na 10 na mambobin kungiyar ciniki ta kasashen duniya WTO, wanda ake gudanarwa a birnin Nairobin kasar Kenya, a jiya Laraba ya amince da ayyana kasar Liberiya a matsayin mamba a kungiyar, bayan shafe tsawon shekaru 8 ana kokarin cimma daidaito kan lamarin.

A jawabinta na bude taro, shugabar kasar Liberiya Ellen Johnson Sirleaf ta ce, amincewa da Liberiya ta zama mamba a WTO wani muhimmin al'amari ne mai dunbun tarihi, a daidai lokacin da kasar ke kokarin farfadowa bayan halin matsi da ta fada sakamakon bullar cutar Ebola a shekarar da ta gabata.

Liberiya ta kasance kasa ta 163 ciki jerin kasashe mambobin kungiyar WTO, kuma ita ce kasa ta 35 mafi koma baya ta fukar cigaba, cikin jerin kasashe mambobin kungiyar.

Sirleaf ta jaddada aniyar gwamnatin ta fuskar siyasa da tattalin arziki, wajen inganta sha'anin tattalin arzikin kasar.

Ana sa ran shigar Liberiyar cikin kungiyar WTO, zai janyo hankalin masu zuba jari a fannin tattalin arzikin kasar.

Shugaba Sirleaf ta ce, gwamnatin kasar ta tanadi kyakkyawan yanayi ga masu zuba jari a kasar a fannonin makamashi, da sufuri, da kayayyakin more rayuwa, da yawan bude ido da kuma harkar noma.

Babban daraktan kungiyar WTO Roberto Azevedo, ya bayyana cewa kasar Liberiya ta samu nasarar zama mamba a WTO ne, sakamakon irin rawar da take takawa a hulda da kasashen duniya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China