in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci ministocin cinikayya da ke taron WTO da su mayar da hankali ga batun samar da abinci
2015-12-16 10:00:16 cri
Jami'in musamman na MDD mai kula da samar da abinci Hilal Elver ya yi kira ga ministocin cinikayya da ke halartar taron kungiyar cinikayya ta duniya a kasar Kenya ko WTO a takaice da su mayar da hankali wajen ganin sun aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma game da harkokin cinikayya.

Jami'in na MDD na bayyana hakan ne a jajiberen taron ministocin karo na 10 da zai gudana daga ranar 15 zuwa 18 ga wannan wata na Disamba. Yana mai cewa, wajibi ne dokokin cinikayyar su kartata ga manufofin samar da abinci wadanda za su dace da kasashe masu tasowa, maimakon manufofin da za su rika magana kan dokokin kungiyar ta WTO kawai.

Ya ce, muddin ana bukatar samar da abinci, to, wajibi ne a gaggauta yi wa dokokin kungiyar game da aikin gona gyaran fuska. Ya kuma tunatar da mahalarta taron na birnin Nairobin Kenya game da yarjejeniyar da aka cimma tun a shekarar 2008, da kuma wadda aka cimma a Bali na kasar Indonesia a shekarar 2013 game da karancin wasu abubuwa na ci gaba, ciki har da yadda ake tafiyar da harkokin cinikayya.

A hannu guda jami'in na MDD ya nuna damuwa game da kiraye-kirayen da wasu masu shiga tsakani ke yi kan a dakatar da tattaunawar da ake kan ajandar taron Doha.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China